Al’umma su sanar da mahukunta duk wani motsin bata gari da basu aminta da shi ba- Brigediya Mai Aduwa

Kwamitin kar-ta-kwana na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kwacen waya na jihar kano ya…

Zamu haɗa hannu da kamfanoni domin samar da ma’adanai a kano – Kwamishina Kachako

Gwamnatin jihar kano ta ce zata ci gaba da haɗa hannu da kanfanoni masu zaman kansu…

Gwamna Yusuf Ya mika sakon Ta’aziyya ga Gwamnatin Bauchi bisa rasuwar Sarkin Ningi.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai da gwamnatin jihar Bauchi…

Shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke shugaban hukumar tsaron farin kaya (DSS), Yusuf Bichi.

  Kakakin shugaban ƙasa Ajuri Nglale ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da…

An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano bisa Taimakawa Daliban karamar hukumar Dawakin Tofa

  Kungiyar Daliban karamar hukumar Dawakin Tofa da asusun tallafawa ilimi na karamar hukumar Dawakin Tofa…

Abun da Mahukuntan Nigeria ke yiwa Matatar mai ta Ɗangote ka iya yiwa tattalin arzikin kasar illa-Falakin Shinkafi

Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya kalubalanci hukumomin man fetur na Nigeria Saboda kokarin zagon kasa da suke yiwa matatar man fetur ta Ɗangote wadda yace hana ta aiki tamkar hana talaka samun sauki ne.

Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Manema labarai a ranar talata.

Ya ce a kwanan baya gwamnatin tarayya har karya darajar naira ta yi saboda masu zuba hannun jari na kasashen waje, amma abun mamaki ga dan kasa ya kashe magudan kudadensa maimakon a taimakasa kuma a gode masa amma an zo ana bin sa da bita da kulli.

” Wannan matatar man ta Ɗangote babu shakka ita ce matatar mai mafi girma a Africa Kuma Allah ya taimake mu dan kasar mu ne mai ita, kyautuwa ya yi gwamnatin tarayya ta ba shi dukkan wata gudunnawa don ya yi nasara, domin idan ya yi nasara tattalin arzikin Nigeria ma ya yi nasara domin zai kara bunkasa”. A cewar Falakin Shinkafi.

Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bukaci gwamnatin tarayyar Nigeria da ta takawa wadancan hukumomin man fetur na kasar burke, idan kuma da sanin ta ake haka to ta sani yan Nigeria ba za su lamunci kawo cikas akan abun da zai kawo musu sauki ba.

” Bawan Allah nan ya zo ya yi wannan matatar domin tace man fetur da Gas da sauransu don yan Nigeria su sami sauki amma an zo sai tuhume-tuhumen ake masa, ko karya shi ake so ayi ko so ake ya rufe mu ba mu gane ba, kuma gwamnati Kullum tana cewa yan kasuwar duniya su zo su saka hannun jari a ƙasar ta ya hakan zai yiwu”. Inji Falakin Shinkafi

Falakin Shinkafin wanda shi ne jarman matasan Arewacin Nigeria ya bukataci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan matsalar don cigaban yan kasa da tattalin arzikin Nigeria.

Shugaba Joe Biden, ya janye kudirin sake tsayawa takara.

Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya bar wa mataimakiyarsa, Kamala Harris, tikitim zama ‘yar takarar shugaban…

Ganduje yasa an sauke Sanata Ali Ndume daga kan matsayin bulaliyar majalisar dattawa

Majalisar dattijai ta sauke sanata Ali Ndume daga kan kujerar bulaliyar majalisar sakamakon wasu kalamai na sukar Tinubu da ya yi.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da sakataren jam’iyyar sune suka nemi majalisar ta tsige shi daga kan matsayin.

Kuma batare da wata jayyaya ba, Shugaban majalisar Godswil Akpabio ya baiyana bukatar ta ganduje, a nan take kuma suka nuna amincewar su da daukar matakin, bayan kada kuri’a ta muryar baki.

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sabbin sarakunan da zasu jagoranci masarautun Rano, Gaya da Kuma karaye a matsayin sarakuna masu daraja ta biyu.

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sabbin sarakunan da zasu jagoranci masarautun Rano, Gaya da Kuma karaye a matsayin sarakuna masu daraja ta biyu.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar.

Sarakunan sune Alhaji Muhammad Mahraz Karaye a matsayin Sarkin Karaye Wanda Kafin nadin nasa shi ne Hakim Karamar hukumar Rogo.

Sai Alhaji Muhammad Isa Umar a matsayin Sarkin Rano Wanda Kafin nadin nasa shine hakimin Bunkure.

Da Kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya a matsayin Sarkin Gaya Wanda ya kasance tsohon Sarkin masarautar Gaya wadda aka rushe.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hori sabbin sarakunan masu daraja ta biyu da su zamo masu hada kan al’umarsu da tabbatar da zaman lafiya da kuma bunkasa al’adu a masarautunsu daban daban.

Sanarwar tace nadin nasu ya fara aiki ne nan take.

Abba Kabir Yusuf ya rabawa Ma’aikatan gidan gwamnati Babura

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rabawa wasu daga cikin Ma’aikatan gwamnati Babura Masu kafa…