Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya

Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya

Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya
Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya

Shugaban ƙasan Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ƴanwasan tawagar Super Eagles maraba da dawowa Najeriya bayan matsalar da suka fuskanta, sannan ya buƙaci a gaggauta bincike,

tare da tabbatar da hukunci na adalci game da tirka-tirkar da ta faru da ƴanwasan Super Eagles a Libya.

Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

Tinubu ta buƙaci kwamitin ladabtarwa na CAF, “ta yi bincike, sannan ta bayar da shawarwarin irin hukuncin da ya kamata a ɗauka a kan waɗanda suka saɓa ƙa’idoji da dokokin hukumar.”

Shugaban ya kuma yaba da ƙoƙarin ma’aikatar harkokin ƙasashen waje da ma’aikatar wasanni bisa ƙoƙarin da suka yi wajen shawo kan lamarin.

Haka kuma ya yaba da juriyar da ƴanwasan suka nuna duk da matsalar da suka fuskanta.

A ƙarshe ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa da su yi duk mai yiwuwa domin hana sake aukuwar irin wannan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *