Shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke shugaban hukumar tsaron farin kaya (DSS), Yusuf Bichi.

 

Kakakin shugaban ƙasa Ajuri Nglale ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Shugaban ya maye gurbinsa da Adeola Oluwatosin Ajayi.

Kazalika, shugaban ya naɗa Mohammed Mohammed a matsayin shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA) domin ya maye gurbin Ahmad Rufai Abubakar, wanda ya ajiye aikinsa a ƙarshen makon da ya gabata.

Mista Adeola dai shi ne mataimakin shugaban hukumar DSS ɗin kafin naɗin nasa a halin yanzu.

Haka kuma Mohammed ya fara aiki da NIA tun 1995, a inda ya yi karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *