Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai da gwamnatin jihar Bauchi bisa rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Muhammad Danyaya wanda ya rasu a ranar Alhamis din da ta gabata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin. A cewar sanarwar, gwamnan ya bayyana marigayi Alhaji Muhammad Danyaya a matsayin daya daga cikin sarakuna da ya jajirce wajen ci gaban masarautarsa ta jihar Bauchi,da ma kasa baki daya.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba da irin gudunmawar da marigayi sarkin ya bayar ta bangaren tsarin mulki na kasa da kuma samar da zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabas wadda ta dade tana fama da rashin tsaro.
A madadin gwamnati da mutanen jihar Kano, gwamnan ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya jikansa da rahama, yasa Aljannar Firdausi ta zamo makoma a gareshi, ya kuma baiwa iyalansa jajircewa da juriyar wannan rashi.”