An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano bisa Taimakawa Daliban karamar hukumar Dawakin Tofa

 

Kungiyar Daliban karamar hukumar Dawakin Tofa da asusun tallafawa ilimi na karamar hukumar Dawakin Tofa sun karrama Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa bisa namijin kokarin da yake yi na ciyar da dalibai gaba a karamar hukumar.

Sunusi Bature wanda shine mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu shaidar karramawar ne yayin wata ziyarar da kungiyar ta kai masa ofishin sa a ranar Talata.

Karramawar na kunshe cikin wata wasikar godiya da Dr. Mamunu Mustapha ya gabatar a madadin kungiyoyin biyu.

Wasikar ta bayyana irin jajircewar da Sunusi Bature ya bayar ga dimbin daliban Dawakin Tofa, musamman daliban dake karatun digiri a Jami’ar Bayero Kano.

Gudunmawar da ya bayar, wadda ta hada da biyan kudaden rajista na zangon karatu na 2023/2024, da shigewa gaba wajen biyawa dalibai matsalolin kudi, Wanda hakan yasu damar mayar da hankali kan karatunsu.

Baya ga tallafin da yake baiwa daliban BUK, Sunusi Bature ya tsallaka zuwa sauran manyan makarantun gaba da sakandire inda ya aiwatar da makamancin wannan tallafi.

Kazalika Sunusi Bature ya bayar da irin wannan tallafi ga daliban Makarantar fasaha d Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano da ke Gwamai, tare da kara fadada hanyoyin samun ilimi ga matasa a karamar hukumar.

Kungiyoyin sun jaddada cewa tallafin da Sunusi Bature yake bayarwa wajen inganta harkokin ilimi a Dawakin Tofa ya taimaka matuka wajen kara samun dalibai masu ci gaba da karatu.

Sun bukace shi da ya ci gaba da kokarinsa na daukaka matsayin ilimi da samar da damammaki ga matasa a cikin al’umma.

A nasa bangaren Sanusi Bature ya ce ya zama wajibi a kansa ya bada dukkanin gudunmawa domin bunkasa ilimi a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *