Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden, ya bar wa mataimakiyarsa, Kamala Harris, tikitim zama ‘yar takarar shugaban ƙasar Amurka, a jam’iyar Democratic, bayan ya sanarwa da cewa ya hakura da shiga zaben.
Wannan matsaya, da shugaba Biden, ya dauka ta biyo bayan wani matsin lamba da yake fuskanta daga masu ruwa da tsakin jam’iyarsa da suke cewa, shugaba Joe Biden, ya hakura tare da jingine kudirinsa, na sha’awar sake zama dan takarar shugaban Amurka a jam’iyar Democratic.
Wannan na zuwa ne, bayan da shugaba Joe Biden, ya gaza kai bantansa, a muhawarar jin manufofin ‘yan takarar shugaban ƙasa Amurka da aka gudanar a ranar 27 ga watan Yuni, tsakanin shugaba Biden, da jam’iyun adawa.
Joe Biden mai shekaru 81 a duniya, zai kammala wa’adin mulkinsa, a ranar 20 ga watan Janairu, 2025.