Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya kalubalanci hukumomin man fetur na Nigeria Saboda kokarin zagon kasa da suke yiwa matatar man fetur ta Ɗangote wadda yace hana ta aiki tamkar hana talaka samun sauki ne.
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Manema labarai a ranar talata.
Ya ce a kwanan baya gwamnatin tarayya har karya darajar naira ta yi saboda masu zuba hannun jari na kasashen waje, amma abun mamaki ga dan kasa ya kashe magudan kudadensa maimakon a taimakasa kuma a gode masa amma an zo ana bin sa da bita da kulli.
” Wannan matatar man ta Ɗangote babu shakka ita ce matatar mai mafi girma a Africa Kuma Allah ya taimake mu dan kasar mu ne mai ita, kyautuwa ya yi gwamnatin tarayya ta ba shi dukkan wata gudunnawa don ya yi nasara, domin idan ya yi nasara tattalin arzikin Nigeria ma ya yi nasara domin zai kara bunkasa”. A cewar Falakin Shinkafi.
Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bukaci gwamnatin tarayyar Nigeria da ta takawa wadancan hukumomin man fetur na kasar burke, idan kuma da sanin ta ake haka to ta sani yan Nigeria ba za su lamunci kawo cikas akan abun da zai kawo musu sauki ba.
” Bawan Allah nan ya zo ya yi wannan matatar domin tace man fetur da Gas da sauransu don yan Nigeria su sami sauki amma an zo sai tuhume-tuhumen ake masa, ko karya shi ake so ayi ko so ake ya rufe mu ba mu gane ba, kuma gwamnati Kullum tana cewa yan kasuwar duniya su zo su saka hannun jari a ƙasar ta ya hakan zai yiwu”. Inji Falakin Shinkafi
Falakin Shinkafin wanda shi ne jarman matasan Arewacin Nigeria ya bukataci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan matsalar don cigaban yan kasa da tattalin arzikin Nigeria.