Jarumi a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa masana’antar tasu cike take da yan bakin ciki da hassada da kuma maciya Amana, domin akwai mutanen da ya taimakesu a cikin sanadin ɗaukakarsu, amma su na gani ana zaginsa basa iya kare shi, dukda sun san cewa abinda ake zaginsa akansa ba gaskiya bane.
Zango ya bayyana haka ne cikin wani fefen bidiyo da ya saki a ranar Lahadi, inda yace mutane irinsu, Falalu Dorayi, Ado Gwanja, Abubakar Sani, Zainab Indomie da sauransu, duk ya taimakesu wasu ma har kyautar Mota ya basu, shi yasa yake jin tsoro akan abinda ya faru da Marigayi Rabilu Musa Ibro da Aminu S Bono, a lokacin da suke raye da kuma bayan rasuwarsu.
Cikin jawabinsa, Zango ya buga misali da Darakta Ashiru Nagoma da kuma tsohon jarumi Bashir Bala Chiroki, wanda yace duk laifin da suka aikata a Kannywood ya kamata a yafe musu, a taimakesu domin sun iya kuma sun bada gudummawa a masana’antar, kuma Allah ma ana yi masa laifi a nemi afuwarsa kuma ya yafe ballantana Kannywood.
A batun zamantakewar aure tsakaninsa da iyalinsa, Zango yace a cikin matan da yayi zaman aure dasu bai fi guda biyu ne suka yi rabuwa bisa wasu dalilai marasa ƙarfi ko kuruciya ba, amma ragowar duk sun aikata masa wasu laifuka da idan ya bayyana su sai an jinjina masa.