Abba Kabir Yusuf ya rabawa Ma’aikatan gidan gwamnati Babura

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rabawa wasu daga cikin Ma’aikatan gwamnati Babura Masu kafa Biyu, domin inganta musu aikinsu da kuma kyautata musu.

Kimanin Ma’aikatan gidan gwamnati 10 ne suka rabauta da Mashinan, wanda gwamnan yayi Alkawarin cewar zai dinga kyautatawa Ma’aikatansa lokaci zuwa lokaci.

Gwamnan ya horesu dasu killace Baburan da aka basu tare kuma da ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Baburan dai an rabasu ne ga Masinjojin gidan gwamnati guda goma 10, wanda sune suka rabauta a wannan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *