Rundunar yan sandan jahar Kano, ta cafke wasu yan Dabar siyasar 54, dauke da muggan makamai da kwayoyi a ranar Idin Sallah, bisa zarginsu da yunkurin hana gudanar da bikin hawan Daushe a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun 2024.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa Nasara Radio a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce rundunar yan sandan ta gano makircin da wasu marasa kishin Kano da zaman lafiya ke kullawa ne ya ba su damar cafke batagarin matasan.
SP Kiyawa, ya ce daman hukumomin tsaron jahar suna sane da yadda wasu ke shirin ke shirin tayar da hankulan al’umma, inda ya ce akwai isassun jami’an tsaro da na’urorin da za su dinga ba su bayanan yadda abubuwa suke kasancewa a wurare daban-daban.
Rundunar yan sandan ta lashi takobin kama duk wanda ya yi yunkuri kawo rashin zaman lafiya da jahar ke ciki don ya fuskanci hukunci tare da ma su daure mu su gindi.
Kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce bukin hawan Daushe waje na nuna Al’adun Baushe, ba waje na harkokin siyasa ba, da magoya ke nuna fastocin siyasa da alluna, inda ya shawarce su da su kiyaye aikata hakan don ba daidai ba ne.
Mutane 54 da rundunar ta cafke a ranar sallar Idi , suna ci gaba da amsa tambayoyi kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.